'Shugaban Burundi zai iya yin tazarce'

Hakkin mallakar hoto Gahuza
Image caption Pierre Nkurunziza ya sha alwashin ba zai tsaya takara a karo na uku ba.

Kotun tsarin mulkin Burundi ta amince shugaba Pierre Nkurunziza ya tsaya takara a karo na uku.

A shekarar 2005 Shugaba Nkurunziza ya amince ba zai yi takara a karo na uku ba a lokacin wata yarjejeniya da aka kulla wacce ta kawo karshen yakin basarar da aka kwashe shekaru ana yi.

Sai dai daga baya ya sauya wannan matsayin, lamarin da ya janyo mummunar zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Alkalin kotun ya fice daga kasar kwanaki kadan gabanin yanke hukuncin.

Sylvere Nimpagaritse ya ce ya dauki matakin ne saboda yana fuskantar matsin lamba daga hukumomin kasar, ciki har da yunkurin hallaka shi, domin ya amince shugaba Nkurunziza ya tsaya takara a karo na uku.