CAR: An cimma yarjejeniya a Geneva

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Catherine Samba-Panza

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya- UNICEF, ya ce dukanin kungiyoyi masu rike da makamai a jamhuriyar Afrika ta tsakiya sun amince su saki duk yaran da suka tilasta wa shiga aikin soja.

A birnin Geneva ne, aka sanar da matsayar bayan mako guda, da aka shafe ana tattaunawa tsakanin bangarorin a Bangui babban birnin kasar.

Wakiliyar BBC ta ce asusun na UNICEF ya yi ammanar cewa kungiyoyi masu rike da makamai sun dauki yara dubu shida zuwa dubu goma da suka rika aiki a matsayin soja ko masinja ko masu girki kuma an rika lalata da wasu daga cikinsu.

Asusun ya nemi a yi amfani da jadawali mai tsauri, da zai ba yaran damar sake hadewa da iyalinsu.