2015: PDP za ta yi nazari kan rashin nasararta

Hakkin mallakar hoto state house
Image caption Manyan jam'ian PDP sun ce makusantan shugaba Jonathan ne suka sa jam'iyyar ta sha kaye a zabukan 2015.

A Nigeria, ranar Talata ne jam'iyyar PDP za ta kaddamar da wani kwamiti na musamman wanda zai yi nazari a kan halin da ta tsinci kanta a ciki sakamakon kayen da ta sha a manyan zabukan da aka gudanar.

Ana sa ran kwamitin -- karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar Sanata Ike Ekweremadu -- zai gabatar da shawarwari a kan yadda za a farfado da jam'iyyar, bayan kayen da ta sha a hannun jam'iyyar APC.

Jam'iyyar PDP -- wacce ta fara mulkin a Najeriya tun daga shekarar 1999 -- ta rasa kujerar shugabancin kasar da rinjayen da take da shi a zauren majalisun dokokin kasar da kujerun gwamnoni.

Tun bayan zabukan dai, jam'iyyar ta PDP ta fada cikin rikici tsakanin manyan jami'anta da kuma masu goyon bayan shugaban kasar, Goodluck Jonathan.

Su dai masu goyon bayan shugaban sun ce jam'iyyar ta sha kaye ne saboda kafar-ungulun da manyan jami'anta suka yi a lokutan zaben.

Sai dai shugabannin jam'iyyar sun ce jam'iyyar ta sha kaye ne saboda zage-zagen da makusantan shugaban kasar suka rika yi wa Janar Muhammadu Buhari, dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar APC wancan lokacin, maimakon su mayar da hankali kan batutuwan da za su kawo ci gaban kasar.