Kerry ya ziyarci Somalia

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mr Kerry da shugaba Sheikh Hassan Mahmood

Sakataren harkokin waje Amurka, John Kerry ya kai ziyara a Mogadishu babban birnin kasar Somalia.

Ya tattauna da shugaba Hassan Sheik Mohamud da shugabbani yankuna da kuma kungiyoyi fararen hula.

Shi ne sakataren harkokin waje na Amurka na farko da ya kai ziyara kasar.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta ce kasar na son ta isar da alama mai karfi ga mayakan kungiyar Al-shabaab a kan cewa ba ta juya wa kasar baya ba.

Amurka ta bai wa Somalia miliyoyin daloli a shekarun baya bayanan.

Haka kuma jiragen sama marasa matuka na Amurka sun kashe shugabbanin kungiyar ta Al shabaab da dama.