An kashe mutane 20 a sabon rikici a Taraba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kawo yanzu 'yan sanda ba su ce komai ba a kan batun

Rahotanni daga jihar Taraba sun ce an kashe mutane a kalla 20 a wani tashin hankali mai nasaba da kabilanci.

An yi rikicin ne tsakanin kabilar Kuteb da ta Tibi da ke kananan hukumomin Takum da kuma Ussa.

Bayanai sun ce an shafe kwanaki biyu ana tashin hankalin, lamarin da ya janyo hasarar dukiya mai dinbin yawa.

Rahotanni sun ce an soma rikicin ne bayan da ake zargin wasu da kashe mutane biyar 'yan kabilar Kuteb.

'Yan kabilar Kuteb na zargin Tibi da aika ta kisan abin da ya sa suka dauki fansa.

Jihar Taraba ta sha fama da matsalar rikici mai nasaba da addini da kabilanci.