Haihuwa a Amurka na da matsala

A takaice: Matan Amurka sun fi mutuwa a wajen haihuwa fiye da kowace kasa mai arziki.

A Amurka sai a samu masu cikin da suka rasu wurin haihuwa sau goma ba a samu daya a kasar Belarus ba.

Wani rahoto na kungiyar agaji ta duniya "Save the Children," ya gano cewa mata sun fi mutuwa lokacin haihuwa a Amurka fiye da wasu kasashe masu irin arzikin ta.

A cikin rahoton mai taken "Yanayin da mata ke ciki a duniya a shekarar 2015," ya nuna cewa mata a Amurka sun fi mutuwa sakamakon daukar ciki fiye da kasashe irinta kamar Austria ko kuma wadanda ba su kai ta arziki ba kamar su Poland ko Belarus.

A cewar kungiyar kasashen da suka ci gaba ta OECD, Amurka ita ce ta hudu cikin jerin kasashen da suka fi arziki a duniya, yayin da ta zamo ta 33 a rahoton kungiyar Save the Children.

Kungiyar Save the Children ta yi amfani da al'kalumanta a kan lafiyar mata da mutuwar kananan yara da ilimi da tattalin arziki da kuma shigar mata siyasa.

'Birni ma fi matsala'

Birnin Washington DC shi ne wanda aka fi samun hadarin yawan mutuwar jarirai daga cikin manyan biranen kasashe masu arziki 25.

An samu kashi shida da digo shida na mace-mace cikin jarirai 1,000 da aka haifa a shekarar 2013 - wanda hakan yafi karanci a kasar Columbia, amma kuma ya dara na birnin Stockholm da Tokyo har sau uku.

Rahoton ya nuna cewa yaran da suke yankunan da suka fi fama da talauci sun fi mutuwa tun kafin su shekara daya a duniya fiye da tsararrakinsu da ke yankunan da suka fi arziki.

Ya jaddada cewa irin tazarar da ake samu tsakanin talakawa da masu arziki a manyan birane na da nasaba da yadda yawan mutane ke karuwa a biranen.

Image caption Sheila mai shekaru 20 a birnin Nairobi na Kenya

'Tazara tsakanin masu kudi da talakawa'

Rahoton ya yaba nasarar da aka samu wurin rage mutuwar mata da jarirai a manyan birane kamar su Kampala da Addis Ababa.

Amma a wasu wuraren masu kudi ne suka fi morar duk wasu harkokin jin dadi inda ake samun tazara mai yawa tsakanin hanyoyin more rayuwa na mai kudi da talaka.

A yawancin kasashe, 'ya'yan talakawa da ke rayuwa a birane sun fi mutuwa fiye da tsararrakinsu 'ya'yan masu hali. An gano cewa an fi samun irin wannan ratar rayuwa da ke tsakanin yaran birni a kasashe irin su Bangladesh da Ghana da Indiya da Kenya da Najeriya da Peru da Biyatnam da sauran kasashe irin su.

Shugabar kungiyar agaji ta duniya "Save the Children" Jasmine Whitbread, ta ce "Ga jariran da ake haifa a mafi yawan biranen da ke bunkasa a duniya kuwa, wadanda suka fi rayuwa a cikinsu su ne 'ya'yan masu kudi."

Haka kuma birnin Alkahira na Masar da birnin Guwatamala sun yi kokari wajen rage mace-macen yara kanana inda aka samu banbanci kadan tsakanin masu arziki da talakawan biranen.

Hakkin mallakar hoto save the children

Rana da 'ya 'yanta biyu suna rayuwa ne a tsakiyar biranin New Delhi na kasar Indiya, amma ba su da wutar lantarki ba ruwan famfo ba bandaki

'Zaki da madaci'

Kasashen da suka fi magance matsalar mutuwar kananan yara a birane sune kasashen da ke arewacin Turai irin su Finland da Iceland da Denmark da kuma Sweden.

25 daga cikin kasashe 30 da suka fi yin hobbasa don magance wannan matsala a Turai suke.

Kasashen da aka fi yake-yake a Afrika sune wadanda ba sa yin wani abin a zo a gani domin magance matsalar yawan mutuwar yara, kamar su Mali da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da Jamhuriyar Dimokradiyar Kongo da kuma Somaliya.

Wadannan su ne jerin kasashen da aka lissafa a shekara ta 2015

1. Nowe 7. Sipaniya 14. Singapo 24. Birtaniya 33. Amurka 36. Ajantina 53. Mekziko 56. Rasha 61. China 65. Turkiya 73. Labanan 77. Barazil 83. Tailan 84. Iran 90. Azarbajan 92. Sirilanka 98. Biyatnam 100. Iraki 111. Sitiya 112. Indonesiya 114. Nepal 116. Masar 118. Uzubekistan 130. Bangaladash 138. Kenya 140. Indiya 149. Pakistan 152. Afganistan 173. Kwat Di buwa 178. Jamhuriyar Dimokradiyar Kongo 179. Somaliya