APC ta soki nadin mukaman Jonathan

Image caption A ranar 29 ga watan Mayu jam'iyyar APC za ta karbi ragamar mulki a Nigeria

Jam'iyyar APC a Nigeria wacce dan takararta zai dare karagar mulkin kasar daga ranar 29 ga wannan watan, ta ce tana kallon nade-naden mukaman da shugaba Jonathan din ke yi a baya bayan nan a matsayin wani yunkuri na lalata tsarin da jam'iyyar ta shimfida na tafiyar da mulkin kasar.

Wani jigo a jam'iyyar, Sanata Lawal Shuaibu, ya bayyana cewa mataki ne da sam dai dace ba.

Ya ce "gwamnatin da bata da kudi mai ya kai ta dibar ma'aikata".

Shugaba Jonathan dai a baya bayan nan, ya sauke wasu masu rike da mukamai da kuma maye gurbinsu da wasu.

Fadar Shugaban Kasar bata bayyana dalilin da ya sa take gudanar da wadannan nade-nade ba.