Ana kammala yakin neman zabe a Biritaniya

Image caption Shugabannin jam'iyyu a Burtaniya

A ranar Laraba ne 'yan siyasa a Biritaniya suke kawo karshen yakin neman zaben gabanin zaben 'yan majalisar dokoki a ranar Alhamis.

Zaben na ranar Alhamis shi ne mafi zafi tsakanin manyan jam'iyyun kasar, Conservative da Labour.

Su ma kananan jam'iyyu a kasar za su kara sauya lissafin zabukan kasar, inda alamu ke nuna jam'iyyar Scottish National Party za ta zama babbar jam'iyya ta uku a kasar.

Kawo yanzu babu tabbaci a kan ko wacce jam'iyya ce za ta lashe kujeru mafi rinjaye, ganin yadda binciken jin ra'ayoyin jama'a ya nuna babu daya daga cikin manyan jam'iyyun kasar da ta shiga gaba da babbar tazara.

Manyan abubuwan da suka fi daukar hankali a zaben sun hada da ci gaba da kasancewar Biritaniya cikin Tarayyar Turai da kuma tattalin arziki.

Biritaniya dai na bin tsarin shugabanci ne irin na Firai Minista, don haka jam'iyyar da ta samu rinjaye a majalisar dokoki ce za ta kafa gwamnati.