Buhari: Ban yarda da keta dokokin tuki ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Take dokokin titi abune da ake zargin ayarin motocin Shugabanni na yi

A wani mataki da ba kasafai ake ganin irinsa ba a Nigeria, zababben shugaban kasar janar Muhammadu Buhari ya umurci daukacin jami'an tsaron dake kula da tsaron sa, da kuma sauran mukarraban sa, dasu rika mutunta dokokin tuki a duk lokacin da suke zirga zirga da shi.

A wata sanarwa da kwamitin yakin neman zabensa ya fitar, Janar Buhari ya nanata cewa lokaci fa da za'a rika amfani da jami'an tsaro wajen karya doka ko kuntatawa talakawan da basu ji ba basu gani ba ya zo karshe, da zarar ya dare kan karagar mulkin kasar.

Janar Muhammadu Buhari ya kuma bayyana cewa a tsarin mulkin demukradiyya, babu dalilin da zai sa shugabanni su rika kuntatawa 'yan kasa don jin dadin su.

Batun karya dokokin tuki dai wani lamari ne da ya zama tamkar ruwan dare a Nigeria.