Muna cin bashi domin biyan albashi - Iweala

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tattalin arzikin Nigeria ya dogara ne a kan man fetur

Ministar kudin Nigeria, Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce gwamnati na cin bashin kudi domin ta biya albashin ma'aikata saboda mummunan halin da tattalin arzikin kasar ya fada a ciki.

A cewarta, faduwar farashin man fetur a duniya ya sanya tun daga watan Janairun bana zuwa yanzu, gwamnati ta ci bashin fiye da naira biliyan 400.

Iweala ta ce, "Daga cikin naira biliyan 882 da aka amince a karbo bashi a cikin kasafin kudin bana, a yanzu haka gwamnati ta ci bashin naira biliyan 473 domin gudanar da ayyuka da kuma biyan albashi."

Wannan labarin ba zai yi wa gwamnatin Janar Muhammadu Buhari wacce za ta karba mulki a ranar 29 ga watan Mayu ba, saboda kasancewa zai soma mulki ne a lokacin da tattalin arzikin kasar ke tangal-tangal.

Masu sharhi na ganin cewar matsalar tattalin arzikin na da nasaba da irin makudan kudaden da aka kashe lokacin zaben da aka gudanar a kasar a 'yan makonnin da suka wuce.