An samu Salman Khan da laifin kisa a Indiya

Hakkin mallakar hoto agency
Image caption Salman Khan ya yi fice wajen yin fina finai a India

Wani Alkali a Indiya ya samu daya daga cikin taurarin fina finan kasar, Salman Khan, da laifin kisan wani mutum mara galihu a wani hatsarin mota shekaru 13 da suka gabata.

An zargi Mr Khan da kutsa motarsa cikin wani taron jama'a da ke bacci a bakin titin da ke kusa da gidansa a Mumbai, babban birnin kasar.

Wakiliyar BBC a Indiya ta ce Salman ya dage cewa ba shi da laifi, yana mai cewa direbansa za a zarga da laifin domin shi ne ke tuka motar, amma shaidu da dama sun ce ba haka lamarin yake ba.

Alkalin dai ya ce Salman Khan ne ke tuka motar, kuma a buge yake a lokacin da hatsarin ya auku.

Har yanzu dai ba a yanke masa hukunci ba.