Bam ya fashe a sansanin soji a Sudan

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sudan ta taba zargin Isra'ila da kai hare-haren sama a kan wata masana'anta da ake kera makamai

Wani abu da ake zaton bam ne ya fashe a sansanin sojoji a wajen Khartoum, babban birnin Sudan.

Mazauna yankin Omdurman da ke yammacin gabar kogin Nilu sun ce cikin tsakiyar dare sun ji karar fashewar bam, sai kuma suka ji ana kai hare-hare da makamai masu kakkabo jiragen sama.

Wani kakakin gwamnatin Sudan ya tabbatar da cewa dakarun gwamnati sun bude wuta a wasu wurare amma ya karyata cewa an kai wa dakarun nasu hare-hare.

Shekaru uku da suka gabata Sudan ta zargi Isra'ila da kai hare-haren sama a kan wata masana'anta da ake kera makamai a Khartoum.

Isra'ila dai ba ta taba mayar da martani a hukumance ba a kan zargin.