Cameron ya dauki hanyar wa'adi na biyu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fira Minista David Cameron ya kama hanyar komawa fadar 10 Downing Street

Bayan an kwana ana tattara sakamakon manyan zabukan da aka gudanar a Biritaniya, Fira Minista David Cameron na jam'iyyar Conservative ya dau hanyar yin wa'adi na biyu a kan kujerar mulki.

Bayan bayyana sakamakon fiye da rabin mazabu, alamu na nuna cewa yawan kujerun jam'iyyar ta Conservative zai karu, kuma mai yiwuwa ta samu adadin da take bukata ta yi mulki ita kadai.

Da yake jawabi bayan an bayyana sake zabensa a matsayin dan majalisa mai wakiltar mazabar Witney, Mista Cameron ya yi alkawarin cewa, "Ina so jam'iyyata, da ma gwamantin da na ke fatan kafawa ta mai do da wata inuwa wadda bai ma kamata a ce mun rasa ta ba tun farko--inuwar kasa daya, hadaddiyar Burtaniya. Wannan shi ne tsarin gudanar da gwamnatina idan na yi sa'ar kafa gwamnati a kwanakin dake tafe".

Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Labour, Ed Miliband, ya bayyana sakamakon zuwa yanzu da cewa bai yi dadi ba.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jam'iyyar Conservative ta kama hanyar sake lashe zaben Biritaniya.

Karin bayani