Kwastam sun damke wasu 'yan China a Kano

Image caption 'Yan China da dama suna da shaguna a Afrika

Hukumar kwastam a Nigeria ta tsare wasu 'yan kasar China hudu bisa zargin fasa-kwaurin kayayyaki cikin kasar.

Ofishin hukumar da ke Kano, ya ce, an kama tufa da wasu kayayyakin masaku na miliyoyin naira da ake zargin, 'yan Chinar sun shiga da su birnin Kano ba bisa ka'ida ba.

Ba wannan ba ne karon farko da hukumomi a Nigeria ke tsare 'yan China bisa yin kasuwanci a cikin kasar da suka sabawa doka.

A birnin Kano, cibiyar kasuwanci a arewacin Nigeria, 'yan China na hada-hada sosai a kasuwannin birnin musamman kantin kwari inda ake sayar da shaddoji da kuma atamfofi.

Kasar China ce babbar abokiyar kasuwanci ga kasashen Afrika inda a yanzu ta shiga gaban Amurka da kasashen Turai.