Ivory Coast ta haramta amfani da man bilicin

Image caption Mata a kasashen Africa suna amfani da man da ke sanya fatarsu tana kara haske.

Kasar Ivory Coast ta haramta yin amfani da man shafawa da ke kodar da fatar mutane, wato bilicin saboda illar da hakan ke haifarwa ga lafiyar mutane.

Mata -- wasu lokutan ma har da maza -- a kasashen Africa da dama sun kwashe shekara da shekaru suna shafa man a ke kara hasken fata da zummar kara musu kyau.

Sai dai masana harkokin lafiya sun ce yin amfani da man yana janyo cutar sankara tawo cancer da ma wasu cututtukan.

Ana yin amfani da wannan mai sosai a Najeriya.

Kasar Africa ta kudu ta aiwatar da doka mai tsauri a kan amfani da irin wannan mai, har ma ta hana yin amfani da sinadarin hydroquinone, da ke kara hasken fata, ko da yake fiye da kashi uku cikin 100 na matan kasar suna amfani da shi.