Za a yi wa fursunoni riga-kafi a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumomin Nijar sun ce fursunoni sama da dubu goma za a yi wa allurar riga-kafin

Ma'aikatar Shari'a ta Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da wani shiri na yi wa fursunonin kasar allurar riga-kafin kamuwa da cutar sankarau.

Wadansu kungiyoyin farar hula ne dai suka dauki alhakin tattaro gudunmawar da aka yi amfani da ita don tanadin alluran riga-kafin.

Jagoran gamayyar kungiyoyin, Moustafa Kadi, ya ce za a fara riga-kafin ne daga gidan yari na Yamai.

"Ciwo, in ya shiga gidan kaso, yana da matsala kwarai. Kuma su ma 'yan kaso hakkinsu ne a kare su..."

Hukumomin da ke kula da gidajen yari sun da ma suna sa rai gwamnati ta dauki wannan mataki, sai ga shi taimako ya zo daga kungiyoyin farar hula.

A cewar Malam Mamane Sani Oussaini, daraktan ma'aikatar da ke kula da gidajen yarin, "Faduwa ce ta zo daidai da zama.... Gidan kason Yamai ya cika ya batse, har ya fashe ma za a ce, tun da mutum 350 ya kamata ya dauka, amma a yanzu zancen da nake maka muna da 'yan kaso 1,022.

"To ka ga ke nan in mutum ya kamu da cutar nan, dubun nan sai sun kamu".

Fursunoni kimanin dubu goma ne dai ake sa ran yiwa allurar riga-kafin kamuwa da cutar ta sankarau wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane 265 daga cikin dubu uku da dari takwas da hamsin da shidan da suka kamu a fadin kasar.

Karin bayani