Nigeria:Kotu ta dakatar da gyaran kundin tsarin mulki

Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption Ana ja-in-ja tsakanin 'yan majalisa da bangaren shugaban kasa

Kotun kolin Nigeriar ta umarci majalisar dokokin kasar da bangaren shugaban kasa su dakatar da yunkurin sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin kasar.

A watan Afrilun da ya wuce ne gwamnatin Tarayya ta bukaci kotun ta haramta kudurce-kudurcen da majalisar ta cimma a kan sauye-sauye ga kundin tsarin kasar na shekarar 1999.

Tun da farko shugaba Jonathan ya ki sanya hannu a garan bawul din da majalisar ta yi wa kundin tsarin mulkin kasar inda ya ce sai an yi wasu 'yan gyare-gyare kafin ya sanya hannu.

A kan haka ne, majalisar ta yi barazanar amincewa da sauye-sauyen da suka zartar domin su zama doka.

Wannan na daga cikin kalubalen da ke jiran shugaba mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari yayin da ya ke shirin yin rantsuwar kama mulki a karshen wannan watan.