Sojojin Afganistan sun kai wa 'yan Taliban hari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan sa-kai na kasashen waje ne ke taimaka wa 'yan Taliban.

Rundunar sojin Afganistan ta kaddamar da mummunan farmaki mayakan Taliban a garin Kunduz da ke arewa maso gabashin kasar.

An rufe titin da ke zuwa garin, kuma dubun-dubatar mutane sun fice daga garin.

Wani wakilin BBC a Kunduz ya ce ya ji karar harbe harben bindigogi da kuma musayar wuta da makaman atillare daga tsakiyar garin.

Jami'an gwamnatin Afganistan sun ce mayakan sa-kai na kasashen waje da suka sami horo daga kungiyar IS ne ke taimaka wa 'yan Taliban.

An gano gawarwakin mayakan sa-kai 18 cikin su har da mata guda biyu.