Yemen ta bukaci karin sojoji dag MDD

'Yan tawayen Houthi na ci gaba da dannawa duk da lugudan wuta

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan tawayen Houthi na ci gaba da dannawa duk da lugudan wuta

Kasar Yemen ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya data bai wa dakarun kasa na kasashen waje damar daukan matakin gaggawa domin ceto kasar, musanman biranen Aden da Taiz.

'Yan tawayen Houthi suna ci gaba da dannawa a biranen biyu duk da lugudan wuta ta sama da dakarun kawance da Saudiya ke jagoranta.

Takardar da Yemen ta aikewa Majalisar zata iya samar da halataccen uzuri na amfani da dakarun kasa na kasashen waje a kasar.

Dakarun kawance da Saudiyya ke jagoranta ma sun fara lugudan wuta ta sama a Yemen din ne bayan irin wannan takarda da gwamnatin ta aika Maris tana neman agajin kasahen larabawa dake yankin tekun Fasha.

Ministan harkokin wajen Yeman, Reyad Yassin Abdullah ya bukaci dakarun kawancen da Saudiya ke jagoranta da su kara tallafawa a birnin Aden.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry wanda zai halarci tattaunawa a Saudiya a kan rikicin na Yemen ya ce akwai damuwa sosai yadda lamarin ya tabrbare har ake da bukatar daukin jin kai.