'Yan gudun hijira sun yi zanga-zanga a Yola

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban 'yan gudun hijira na cikin mawuyacin hali a Nigeria

Rahotanni daga Yola babban birnin jihar Adamawa na cewa wasu dimbin 'yan gudun hijira sun yi zanga-zangar lumana a sansaninsu.

Sun yi hakan ne domin nuna damuwarsa a kan zargin muzgunawar da jami'an tsaro ke yi musu.

Wadanda su ka yi zanga-zangar dai basa cikin dimbin mata da kananan yara da a aka ceto daga Boko Haram a dajin Sambisa.

'Yan gudun hijirar wadanda ke sansanin matasa masu yi wa kasa hidima watau NYSC, a birnin Yola suna kuma korafin cewa hukumomi basa kula da su yadda yakamata.

Sai dai rahotanni sun ce gwamnan jihar ta Adamawa Bala Ngilari, a wata ziyara da ya kai sansanin a wannan mako, ya yi wa 'yan gudun hijirar alkawarin cewa gwamnati tana kan kokarin ganin an maida su gidajensu.

Mutane fiye da miliyan uku ne suka rasa muhallansu sakamakon rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Nigeria