Cameron zai kammala shirin kafa gwamnati

Hakkin mallakar hoto
Image caption Fira Minista David Cameron zai kafa sabuwar gwamnati

Fira ministan Burtaniya David Cameron zai yi amfani da hutun karshen mako don kammala shirin kafa sabuwar gwamnati bayan da jam'iyyarsa ta yi nasara a manyan zabukan da aka gudanar.

Da karamin rinjayen da jam'iyyar Conservative ta samu a majalisar dokoki dai ba sai ya hada gwiwa da tsoffin abokan aikinsa na jam'iyyar Liberal Democrat a gwamnatin hadaka ba.

Mista Cameron ya jaddada cewa zai cika alkawarinsa yayin yakin neman zabe na gudanar da kuri'ar raba-gardama a kan ko Burtaniya za ta ci gaba da kasancewa mamba a Tarayyar Turai.

Mai magana da yawun shugaban Tarayya Turai Jean-Claude Junker, Margaritis Schinas, ya ce a shirye suke su saurari shawarwrinsa.

"A shirye hukumar Tarayyar Turai take ta yi aiki kafada-da-kafada da sabuwar gwamnatin Burtaniya, kuma a shirye Shugaba Juncker yake ya gana da David Cameron nan ba da jimawa ba", inji Mista Schinas.

Karin bayani