Kotun duniya za ta sa ido a kan Burundi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fatou Bensouda ta ce ofishinta zai dauki duk matakin da ya dace a kan abin da ke faruwa a kasar

Babbar mai shigar da kara ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC, ta ce ofishinta zai sa ido sosai a kan abubuwan da ke faruwa a Burundi, gabanin zabukan da ake shirin gudanarwa a kasar.

Fatou Bensouda, ta ce, ta damu matuka da yiwuwar kazancewar tashe-tashen hankula na baya-bayan nan, kuma abokan aikinta za su rubuta bayanan duk abin da ke faruwa.

A kasar ta Burundi dai ana ta gudanar da jerin zanga-zanagar nuna adawa da shawarar Shugaba Pierre Nkurunziza ta neman shugabancin kasar a karo na uku.

Masu suka sun ce matakin ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar, duk kuwa da hukuncin da wata kotu ta yanke a farkon wannan makon cewa shugaban na da damar yin takara.

Wata gamayyar kungiyoyin 'yan adawa ta ba da sanarwa cewa za a dakatar da zanga-zangar a tsawon yini guda ranar Asabar.