Cameron na murnar lashe zabe a Burtaniya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Cameron zai kafa sabuwar gwamnati

Jam'iyyar Conservatives a Burtaniya na murnar samun nasarar zaben da aka yi inda Firai minista David Cameron ya yi alkawarin shugabanci domin hadin kan kasar.

Firai ministan ya ce yanzu suna da rinjaye a majalisar dokokin kasar a saboda haka jam'iyyarsa ta Conservatives za ta cika alkawuran da ta dauka a lokacin yakin neman zabe.

Cameron ya ce "Ina son jam'iyyata kuma ina fatan jagorantar gwamnatin da za ta sake hada kawunan yankunan kasa a karkashin inuwa guda."

Game da batun yankin Scotland inda jam'iyyar Scotish National Party ta samu rinjaye, Mr Cameron ya ce zai bai wa yankin samun ikon shugabanci mafi girma a duniya.

Manyan kusoshi a jam'iyyun Labour da kuma Liberal Democrats ciki har da sakataren kudi Danny Alexander da kuma mai tsara dabarun yakin neman zabe wato Doughlas Alexander sun rasa kujerun wakiltar yankinsu a majalisar dokokin Biritaniya.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Hakkin mallakar hoto BBC World Service