Boko Haram: Ana haihuwar yara 45 duk wata

Image caption Jarirai 773 aka haifa daga cikin watanni biyar a sansanin 'yan gudun hijira na Kamaru.

A kalla mata 45 ne ke haihuwa duk wata a sansanin 'yan gudun hijira na Minawao da ke lardin arewa mai nisa a Jamhuriyar Kamaru.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta bayyana hakan bayan da ta gudanar da zagaye na biyu na aikin yi wa yaran da aka haifa takardar shaidar haihuwa da kuma tantance karuwar da aka samu na 'yan gudun hijirar da ke sansanin.

Rahoton da hukumar ta fitar ya nuna ya nuna cewa 'yan gudun hijra 36,000 ne a sansanin na Minawawo, an kuma haifi jarirai 773 daga watan Disambar bara zuwa watan Aprilun bana.

Daya daga cikin matan da suka haihu a baya-bayan nan ta shaida wa BBC cewa "matsalolinmu na da yawa, babu sutura, ba a kula da mu sannan kuma ba abincin kirki."

Kusan shekara guda ke nan da aka mayar da 'yan gudun hijirar Najeriya sansanin Minawawo amma har yanzu hukumar da ke kula da su da kuma gwamnatin Kamaru ba su kai ga ci ba wajen biyan bukatun 'yan gudun hijirar.