Kotu ta dakatar da hukuncin da aka yi wa Salman Khan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin Salman Khan da kisan ne a lokacin da ya sha giya.

Babbar kotun birnin Mumbai na Indiya ta dakatar da hukuncin daurin shekaru biyar a kurkuku da wata kotun birnin ta yanke wa jarumin fina-finan kasar, Salman Khan, bayan an same shi da laifin kisan wani mutum a wani hatsarin mota shekaru 13 da suka gabata.

A ranar Laraba ne karamar kotun ta yanke wa Mr Khan hukuncin, koda yake ta bayar da belin sa domin ya samu damar daukaka kara.

Yanzu dai babbar kotun ta tsawaita lokacin da ta ba shi domin ya daukaka kara.

Ana sa ran za a saurari karar da zai daukaka a watan Yuli.

An zargi Mr Khan da kutsa motarsa cikin wani taron jama'a da ke bacci a bakin titin da ke kusa da gidansa a Mumbai, babban birnin kasar, inda ya kashe mutum daya, sannan ya jikkata mutane hudu.