Microsoft zai daina Windows

Hakkin mallakar hoto microsoft
Image caption Microsoft ya ce, hakan ba yana nufin karshen Windows ya zo ba ke nan

Kamfanin Microsoft, ya ce, manhajar Windows 10, ita ce ta karshe a nau'in kwamfutocinsa masu Windows da yake yi.

Wani babban jami'in kamfanin Jerry Nixon, shi ne ya sanar da haka, sai dai kamfanin, ya ce a nan gaba zai inganta manhajar amma dai ba zai sake yin wata sabuwa ta gaba ba.

A wannan makon ne jami'in ya bayyana wannan shiri a taron kamfanin a Chicago.

Kamfanin na Microsoft ya ce, bayanin jami'in ya nuna sauyi a kan yadda, kamfanin yake yin manhajarsa.

Kamfanin ya ce, zuwa yanzu bai yanke shawarar sunan da zai sanya wa manhajar da zai kirkiro bayan Windows 10 din ba, amma dai babu Windows 11.

Microsoft ya kara da cewa yana sane a baya ya ki amfani da sunan ''Windows 9'', a maimakonsa ya yi amfani da Windows 10, domin kauce wa tsarin da ake bi a baya, don nuna alamar kawo sauyi a manhajarsa.

Sai dai ya ce hakan ya jawo masa da kuma masu sayen kayan kamfanin matsaloli da dama.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A duk bayan shekara uku Microsoft yake kirkiro sabuwar manhaja(OS).

Bayan kirkiro duk wata sabuwar manhaja kamfanin yana kashe makudan kudade wajen tallata manhajar, wajen shawo kan jama'a cewa tafi duk wata manhaja ta baya.

Kamfanin ya ce, wannan mataki na daina kirkiro manhajar Windows ba yana nufin Windows ta tsaya ba ke nan, za a ci gaba da inganta ta.

Ya ce za a ga sabanin hakan ne ma, da irin yadda za a rika inganta manhajar ta Windows da sabbin abubuwa na zamani.