Shugaban jam'iyyar Labour ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Cameron ne kadai ya dara a cikin wadannan mutanen uku

Shugaban jam'iyyar Labour, Ed Miliband, ya yi murabus bayan kayen da jam'iyyarsa ta sha a babban zaben Biritaniya.

Jam'iyyar Labour ta gaza yin nasara musamman a yankin Scotland inda jam'iyyar SNP ta lashe galibin kujerun 'yan majalisar dokoki.

Mr Miliband ya ce ya dauki alhakin rashin yin nasarar a zaben.

Shi ma mataimakin Firai Ministan, Nick Clegg, ya sauka daga kujerarsa ta shugabancin jam'iyyar Liberal Democrats saboda jam'iyyarsa ba ta taka rawar-gani ba a zaben.

Mr Clegg ya ce jam'iyyarsa tana bukatar sabon shugaban domin tunkarar kalubalen da ke gabanta a shekaru masu zuwa.

Nigel Farage -- wanda shi ne shugaban jam'iyyar UKIP -- shi ma ya yi murabus saboda kawo yanzu jam'iyyar kujera daya tal ta samu a zaben majalisar dokokin.

Mr Farage, wanda jam'iyyarsa ke yakin neman zabe a kan rage yawan baki a Biritaniya, shi ma ya fadi kujerarsa ta neman zama dan majalisar dokoki.

A yanzu dai ta tabbata cewar Firai Ministan, David Cameron, zai iya kafa sabuwar gwamnati ba tare da gudunmuwar kowacce jam'iyya ba.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service