Shi'a: Ana zaman zullumi a Zaria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sheik Ibrahim Al-Zakzaky ya musanta zargin cewa wasu mazauna unguwar da yake ne suka kai musu hari

Rahotanni daga Zaria a jahar Kadunan Najeriya na nuna cewa ana zaman zullumi a wasu sassa na garin sakamakon wata arangama tsakanin 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi mabiya mazhabin Shi'a da wasu wadanda har yanzu ba a tantance ko su wanene ba.

Bayanai daga garin na nuna cewa wasu mutane sun yi dauki-ba-dadi da 'yan kungiyar ranar Alhamis lokacin da suka kai hari a gidan shugaban kungiyar ta 'yan uwa musulmi Sheikh Ibrahim Al-Zakzaky.

A ranar Juma'a ma an sake arangama da miyagun makamai bayan da maharan suka kara kai farmaki.

Ko da yake babu wata kafa ta hukuma da ta ce uffan dangane da rikicin, Sheikh Ibrahim Alzakzaky ya shaida wa wakilin BBC, cewa su suna kyautata zaton hukumomi ne ke da hannu a hare haren da aka kai musu.