Dalibai uku sun rasu a harin Potiskum

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Boko Haram ta sha kaddamar da hare-hare a Potiskum

Dalibai uku sun rasu sakamakon harin da dan kunar bakin wake da kuma wani dan bindiga suka kai a wata makaranta da ke Potiskum a jihar Yobe.

Bayanai sun ce dan bindigar ya bude wuta ne inda ya harbi wasu dalibai sannan shi kuma dan kunar bakin waken ya ta da bam a wurin ajiye motoci.

Rahotanni sun ce dalibai biyar sun ji mummunan rauni a yayin da wasu kuma suka jikkata a kokarinsu ne tserewa.

Wasu bayanai sun ce an damke dan bindigar inda mutanen gari suka yi masa dukan kawo wuka.

Ana zargin 'yan Boko Haram ne suka kai wannan harin, ta yin la'akari da cewa sun sha kaddamar da hare-hare a Potiskum da kuma wasu garuruwan da ke arewa maso gabashin kasar.

A cikin watannin da suka wuce dakarun Nigeria tare da hadin gwiwar sojojin makwabtan kasashe sun fatattaki mayakan Boko Haram daga galibin manyan garuruwa a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.