Turkiyya: Kenen Evren ya rasu

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Janar Kenan Evren ya mutu yana da shekara 97 a duniya.

Tsohon shugaban kasar Turkiyya Kenan Evren, wanda ya jagoranci wani juyin mulkin da aka zub da jini a shekarar 1980, ya mutu a wani asibiti da ke Ankara, babban birnin kasar.

A bara aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai saboda rawar da ya taka a juyin mulkin da ya fara dora shi kan shugabancin kasar.

A karkashin mulkinsa an zartar wa mutane da dama hukuncin kisa, an kama dubban mutane, an kuma haramta jam'iyyun siyasa tare da kame shugabanninsu.

Wakilin BBC ya ce masu ra'ayin gurguzu, da Kurdawa, da 'yan kishin kasa, da masu kishin Muslunci suna alakanta Kenan Evren da mulkin danniya, kuma mutane da dama ba za su yi alhinin mutuwarsa ba.