Gudun Hijira: Ba za mu yarda da Turai ba —Libya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Matsi a Libya ke sa 'yan gudun hijira kasadar tsallakawa zuwa Turai, inji Amnesty International

Jakadan Libya a Majalisar Dinkin Duniya, Ibrahim Dabbashi, ya ce kasarsa za ta sa kafa ta shure da duk wani yunkuri da Tarayyar Turai za ta yi na samun amincewar Kwamitin Sulhu ta yi amfani da matakan soji a kan masu safarar mutane a tekun Bahar Rum.

Mista Dabbashi ya shaida wa BBC cewa Tarayyar ta Turai ba ta tuntubi gwamnatin Libya ba.

"Muna cikin duhu game da hakikanin manufarsu, da irin matakin sojin da suke so su dauka a cikin iyakokinmu na ruwa, kasancewar Tarayyar Turai ba ta tuntubi gwamnatin Libya ba. Wannan ce damuwarmu", inji Mista Dabbashi.

Nan gaba a yau jami'a mai kula da harkokin waje ta Tarayyar Turai, Federica Mogherini, za ta yi jawabi ga kwamitin sulhu a kan shirin.

A ranar Larabar wannan makon ne ake sa ran Hukumar Tarayyar Turai za ta gabatar da wadansu sababbin shawarwari a kan yadda ya kamata a bullowa matsalar 'yan gudun hijirar.

Shawarwarin sun hada da wani tsari na kayyade adadin 'yan gudun hijirar da dukkan kasashen Turai za su baiwa masauki.

Ana kuma sa ran manufar Hukumar game da 'yan gudun hijira za ta bayar da shawarar samar da halaltatun hanyoyin da 'yan gudun hijirar za su iya bi su je Turai, ko sa daina bin masu safarar mutane.

Ranar Lahadi kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta ce mummunan cin zarafi da ukuba, da fyaden da 'yan gudun hijira ke fuskanta a Libya na cikin dalilan da ke tunzura su su sadaukar da rayukansu a yunkurin tsallakawa zuwa Turai.