Nijar na fama da cunkoson fursunoni

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana dangantaka matsalar da karancin alkalai

Wasu kungiyoyin kare hakin dan adam sun koka da cunkoson da ake fama da shi a gidajen kason Jamhuriyar Nijar.

Kawancen kungiyoyin kare hakkin dan Adam na RASCONI, ya ce, binciken da ya yi ya gano cewa rashin gaggauta shari'a na cikin dalilan da ke janyo cunkoson.

Binciken ya gano cewa, a gidan yarin Yamai wanda ke karbar 'yan kaso 350, yana da kusan mutane 1034 a yanzu.

Sai dai hukumomin shari'ar sun ce sun san da matsalar kuma tuni suka umarci jami'ansu da su dau matakan da suka dace.

Wasu rahotanni sun ce sakamakon cunkoson wasu 'yan kason har suma su ke yi a wannan lokaci na zafi.