SA: Bakar fata ya zama shugaban adawa

Babbar jam'iyyar adawa a Afrika ta Kudu Democratic Alliance ta zabi shugabanta na farko bakar fata.

Wakilai a babban taron jam'iyyar a birnin Port Elizabeth da ke kudu-maso-gabashin kasar sun zabi Mmusi Maimane.

Dan shekaru 34, Mista Maimane shine fitaccen wanda dama ake gani zai gaji shugabar jam'iyyar mai-barin-gado Helen Zille.

Mista Maimane ya bayyana farin cikinsa da zaben nasa da aka yi.

Yace: "Ina so na sanar da dukkaninku a yau cewa na gode kwarai ga wadanda suka zabe ni.

"Amma ko ka kada min kuri'a ko baka kada min ba, mu zo mu hada kai domin ciyar da manufar jam'iyyar mu gaba."

Karin bayani