Crimea: Silar koma bayan dangantaka da Rasha

Wasu sojojin Rasha yayin Fareti Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasu sojojin Rasha yayin Fareti

Angela Merkel ta ce dangantaka tsakanin Rasha da Yammacin Turai ta samu koma-baya ne saboda haramtaccen matakin da Rasha ta dauka na shigar da Crimea a cikin kasarta da kuma fadan da ake gwabzawa a gabashin Ukraine.

A nasa bangaren shugaba Putin yace yarjejeniyar da aka cimma a Belarus game da rikicin 'yan awaren na Ukraine yana nan daram.

Angela Merkel ta ajiye furanni a wajen wani biki a Moscow domin karrama mutanen da suka rasa rayukansu a yakin duniya na biyu shekaru 70 da suka wuce, bayan da sojojin Nazi na kasar Jamus suka yi saranda ga dakarun kawancen.

A London ma an gudanar da makamancin wannan biki, inda sarauniya Elizabeth da manyan 'yan gidan sarautar Ingila tare da Firaministan Birtaniya David Cameron da kuma dubban yan mazsan jiya suka bi sahun wajen taron addu'oi a Westminister Abbey.