Matsalar karancin mai ta ta'azzara a Nigeria

Image caption Dogon layin motoci a gidan mai a Abuja

A Najeriya, jama'a na ci gaba da kokawa da matsanancin karancin man fetur a wasu sassan kasar, lamarin da ya gurgunta harkokin yau da kullum.

Rahotanni sun ce tuni masu motocin haya suka kara farashin kudaden safa, yayin da masu sayar da man fetur ta bayan fage, kakarsu ta yanke saka.

Matsalar wadda aka shafe fiye da makonni biyar a na fama da tasa ana fuskantar dogayen layikan motoci a gidajen mai, har da babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai a yayin da matsalar ke kara kamari, Alhaji Abubakar Mai Gandi Dakingari, na kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu IPMAN ya ce ba laifin su ba ne.

Ya ce manyan 'yan kasuwan da suke sayo tataccen mai daga kasashen waje sune ba sa son sayar wa dillalan na kungiyar IPMAN.