Buhari ba zai kyale mu ba —Jonathan

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Goodluck Jonathan ya bukaci ministoci da masu ba shi shawara cewa su shirya domin Janar Buhari zai gallaza musu.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce shugaba mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari, zai gallaza masa idan ya karbi mulki.

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin da yake yin bikin ban-kwana da mulki a wani coci da ke Abuja, babban birnin kasar.

Mr Jonathan ya kara da cewa abokansa da sauran makusantansa sun guje shi tun bayan shan kayen da ya yi a zaben shugaban kasar da ya gabata.

Shugaba Jonathan ya ce, "Ina tausaya wa ministoci da masu ba ni shawara saboda za a gallaza muku. Don haka dole ne ku shirya domin fuskantar hakan".

Ana zargin wasu daga cikin jami'an gwamnatin shugaba Jonathan da hannu a cin hanci da rashawa, kuma shugaba mai jiran gado, Janar Buhari ya sha alwashin cewa zai yi yaki da cin hanci da rashawar.

A kwanakin baya ma sai da Janar Buhari ya ce zai gudanar da bincike kan $20bn da tsohon shugaban babban bankin kasar, kuma Sarkin Kano a yanzu, mai martaba Muhammadu Sanusi II ya ce kamfanin man fetur na kasar bai sanya a asusun bankin ba.