Sabuwar girgizar kasa ta hallaka mutane 40 a Nepal

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Al'ummar Nepal sun shiga cikin zullumi

Mummunar girigizar kasa ta sake auka wa gabashin Nepal, kusa da tsaunin Everest inda mutane akalla 40 suka rasu.

Hakan na zuwa ne makonni biyu bayan girgizar kasa da ta hallaka fiye da mutane 8,000 a kasar.

Hukumomin bayar da agaji sun ce a kalla mutane hudu sun mutu, yayin da mutane da dama suka samu raunuka.

Girgizar kasar ta auku ne a kusa da garin Namche Bazaar, kusa da tsaunin Everest.

Masana kan girgizar kasa sun ce girgizar da ta auku ta kai karfin maki 7.3.

Lamarin ya tilastawa dubban mutane ficewa daga gidajensu inda suka bazama a kan manyan hanyoyi a Kathmandu babban birnin kasar.

An ji girgizar har a cikin India mai makwabtaka da Nepal, a yayinda wasu gine-gine a Delhi suka motsa.

Girgizar kasar da ta auku a ranar 25 ga watan Afrilu, a yammacin kasar, na da karfin maki 7.8.