Umunna na son ya zama shugaban jam'iyyar Labour

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mahaifin Chuka dan Nigeria ne

Dan majalisar dokokin Biritaniya Chuka Umunna ya sanar da cewa zai tsaya takarar shugabancin jam'iyyar Labour.

Mahaifin Umunna dan Nigeria ne daga kabilar Ibo sannan mahaifiyar sa 'yar asalin yankin Ireland ce.

Mr Umunna mai shekaru 36, ya ba da sanarwar ne a wani sakon bidiyo da ya wallafa shafinsa na Facebook, bayan tattaunawa da wasu 'yan jam'iyyar a birnin Swindon.

Dan majalisar wanda ke wakiltar mazabar Streatham wanda aka zaba tun a shekara ta 2010, shi ne mutum na biyu da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara domin maye gurbin Ed Miliband wanda ya yi murabus a makon da ya wuce.

Tuni Liz Kendall ta bayyana cewar za ta yi takarar shugabancin jam'iyyar Labour a yayinda ake sa ran Yvette Cooper, Andy Burnham da kuma Tristram Hunt duk za su nemi kujerar shugabancin jam'iyyar ta Labour.