An cimma matsaya kan Jamhuriyar tsakiyar Afrika

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Catherine Samba Panza shugabar Jamhuriyar tsakiyar Afrika

An samu cimma matsaya a kan batutuwa da dama bayan taron sasanta wa da juna a Jamhuriyar tsakiyar Afrika.

Daga cikin abubuwan da aka cimma an samu bangarorin da suka yafe wa juna sannan kuma gwamnati da kungiyoyin mayakan sa kai sun sa hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta.

Sai dai kuma rahotanni sun ce an watse daga taron cikin tashin saboda an yi ta jin harbe-harben bindigogi kusa da majalisar dokokin kasar inda aka gudanar da taron.

Masu aiko da rahotanni sun ce hakan ya faru ne sakamakon rashin jin dadin wani bangare game da yadda ayyuka suka dinga faruwa.

An kwashe tsawon mako guda ana tattauna makomar kasar a wajen taron.

Sai dai kuma duk da haka an samu cinma matsaya akan batutuwa da dama.