Motoci 4 masu tuka kansu sun yi hadari

Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Mota mai tuka kanta da kamfanin Google ya kera

Ma'aikatar kula da sufurin motoci ta Amurka ta ce hudu daga cikin motoci masu tuka kansu 48 da ake amfani da su a California sun yi hadari a cikin watanni 8 da suka wuce.

A cikin watan Satumban 2014 ne ma'aikatar ta fara bayar da lasisin yin gwajin motocin.

Uku daga cikin motocin hudu da suka yi hadarin mallakin Google ne, cikon ta hudun kuwa, mallakin wani kamfani ne a Delphi.

Sai dai duk kan kamfanonin biyu sun musanta cewa motocin nasu suna da matsala kafin hadarin.

A karkashin dokokin California, ana sirrinta bayanan da suka shafi yadda hadura suke aukuwa.

Google ya ce "muna dora fifiko ga kariya daga hadura. Tun da muka fara kera motoci masu tuka kansu shekaru shida da suka wuce, mun yi tafiyar kimanin mil miliyan daya a manyan hanyoyi da kuma kanana batare da samun hadari ba".

Kamfanin na Delphi ya ce su ma motar su, tana tsaye aka buga mata. Kuma a lokacin, akwai direba a cikin motar, ba ita take sarrafa kanta ba.