An kai karar Nigeria a kan 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan gudun hijirar da sojojin Najeriya suka ceto daga Sambisa.

Wata kungiyar kare hakkin bil adama da ke birnin Lagos a Najeriya SERAF, ta kai karar gwamnatin kasar kotu a kan zargin cin zarafin 'yan gudun hijira da ke kasar.

Kungiyar ta shigar da karar ne a kotun Majalisar Dokokin kasashen yammacin Africa wato ECOWAS, inda ta ke zargin gwamnatin Najeriya da nuna halin ko in kula ga halin da 'yan gudun hijirar ke ciki.

A cewar kungiyar, gwamnatin Najeriyar ta rufe sansanonin da aka kafa domin kula da 'yan gudun hijirar, tana mai cewa hakan ya saba wa doka.

Yawancin mutanen da ke gudun hijirar sun tsere daga gidajensu ne sakamakon hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai musu.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce kungiyar Boko Haram ta kashe fiye da mutane 13,000 yayin da ta raba fiye da mutane miliyan uku daga gidajensu tun daga shekarar 2009, lokacin da ta fara kaddamar da hare-hare a arewacin Najeriya.