An kashe minista a Korea saboda rashin ladabi

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaban Korea ta Kudu Kim Jong-un

Hukumar leken asirin kasar Korea ta Kudu ta ce gwamnatin kasar Korea ta Arewa ta kashe ministan tsaronta Hyon Yong-Chol.

An kashe Mista Yong-Chol ne a gaban daruruwan jami'an gwamnati ta hanyar bude masa wuta da bindigar harbo jirgin sama bisa zargin sa nuna rashin ladabi da biyayya ga shugaban kasar.

Mista Yong-Chol -- a matsayinsa na ministan tsaro -- yana da kusanci sosai da shugaban kasar, Kim Jong-un.

Irin wannan mummunar hanyar kashe ministan wani mataki ne na gargadin jama'a su san hukuncin nuna wa shugaban rashin ladabi da biyayya.

Hukumar leken asirin ta Korea ta Kudu ta ce ana yawaita kashe manyan jami'an gwamnati a kasar Korea ta Arewa, inda ake kashe akalla mutun guda a kowanne mako.