Martabar Nigeria ta dawo a duniya - Blair

Hakkin mallakar hoto Buhari Campaign
Image caption Janar Buhari da Mr Blair

Tsohon Firayi Ministan Biritaniya, Tony Blair ya ce martabar Nigeria ta dawo a idon duniya, sakamakon yadda aka gudanar da zabe a kasar.

Mr Blair ya bayyana haka ne a lokacin ziyarar taya murna ga shugaban Nigeria, mai jiran-gado, Janar Muhammadu Buhari a kan nasarar da ya samu a zaben da aka yi.

A cewar Blair akwai kalubale sosai da ke gaban gwamnati mai jiran gado amma dai idan har aka samu taimaka jama'a to gwamnati za ta iya magance matsalolin.

A nashi bangaren, Janar Buhari ya ce ya ji dadin ziyarar ta Mr Blair kuma sun tattauna yadda Amurka da Biritaniya za su ci gaba da taimakon Nigeria domin ta samu nasara.

Janar Buhari ya ce 'yan Nigeria sun nuna wa duniya cewa demokuradiyya ta zauna daram a kasar.

A karshen wannan watan ne za a rantsar da Janar Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban Nigeria.