Sojoji sun kafa dokar hana fita a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin Najeriya a Maiduguri

Rundunar Sojin Najeriya ta sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a Maiduguri na jihar Borno sakamakon yunkurin kai hare-haren 'yan Boko Haram.

Rahotanni sun ce wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai hari a kusa da birnin Maiduguri da yammacin ranar Laraba.

Kakakin rundunar sojin Nigeria, Kanal Sani Usman Kuka-sheka, ya shaida wa BBC cewa an sanya dokar hana fitar ne domin fatattakan 'yan bindiga da suke neman kaddamar da hare hare a birnin.

Kanal Kukasheka ya ce sojoji sun dakile yunkurin kai harin na yammacin Laraba.

Ya bukaci jama'ar Maiduguri da su mutunta dokar sannan su taimaka wa jami'an tsaro yadda za a samu nasarar murkushe 'yan kungiyar Boko Haram.

Wasu mazauna birnin sun ce koda yake dokar za ta takura wa jama'a, amma tana da muhimmanci domin kare rayukansu.