Fada ya kazanta a Burundi

Masu zanga zangar kin jinin shirin Shugaba Nkurunziza na zarcewa a kan mulki

Asalin hoton,

Bayanan hoto,

Masu zanga zangar kin jinin shirin Shugaba Nkurunziza na zarcewa a kan mulki

An yi musayar wuta sosai a babban birnin Kasar Burundi Bujumbura, inda akai yunkurin hanbarar da Shugaba Pierre Nkurunziza.

Fada ya kazance a tsakiyar Bujumbura, kuma mazauna yankin sunce an soma artabun ne a kusa da gidajen radiyo da talabijin, kuma fadan na ci gaba da yaduwa.

Magoya bayan shugaban Burundin sun ce sun dakile yunkurin juyin mulkin, amma shugaban kasar ya makale a Tanzania, inda yake halartar wani taron kasashen Yankin

Wakiliyar BBC a Burundi tace da alamu an samu rabuwar kawuna a cikin rundunar sojin kasar, don haka ba a san wa ke da iko da kasar ba.

An soki Mista Nkurunziza saboda neman yin tazarce karo na uku a kan mulki, al'amarin da ya haifar da mummunar zanga zanga a kasar.