Japan ta hana amfani da jirgi maras matuki

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a ci wadanda suka karya dokar tarar Fam 265

Kasar Japan ta hana amfani da kananan jiragen sama marasa matuka a wuraren shakatawa dake cikin birane bayan an gano irin jirgin makale a saman gidan Firayiministan kasar.

Kafafen yada labarai na kasar Japan sun ce gwamnati ta hana amfani da jiragen marasa matuka a wuraren shakatawa na gwamnati 81 dake babban birnin kasar.

Rahotannin sun ce duka wanda ya karya wannan hani da aka yi, za a ci shi tarar fam 265.

An kama wani mutun guda saboda samun karamin jirgin a saman gidan Firayiministan kasar.

Mutumin Yasuo Yamamoto mai shekaru 40, ya yi korafi a kan manufofin gwamnatin kasar a game makamashin nukiliya.

'Yan sandan Tokyo suka ce amfani da kananan jiragen a wuraren shakatawan yana da hadari ga yara kanana.