An kafa dokar hana fita a wasu yankunan Filato

Hakkin mallakar hoto plateau state govt
Image caption Jihar Filato ta yi fama da rikice rikice a baya

Hukumomi a jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya sun kafa dokar hana fita a yankunan kananan hukumomi bakwai a jihar.

Hukumomin sun dauki matakin ne sakamakon ta’azzarar da tarzoma ke yi a yankunan a 'yan ‘yan kwanakin nan saboda hare-haren ‘yan bindiga musamman a kauyuka.

Dokar za ta soma aiki ne kama daga karfe 10 na dare zuwa karfe 5 na asuba a kowacce rana.

A makon jiya kadai, an sace dabbobi kimanin 1000 musamman a karamar hukumar Wase, yayin da a kananan hukumomin Barkin Ladi da Riyom da Jos ta Gabas kuma aka kashe mutane masu yawa da kuma kona dukiya, ciki har da gidajen jama’a.