Afrika na can baya a fannin ilimi a duniya

Image caption Wasu dalibai 'yan makaranta a Afrika

An wallafa yadda darajar makarantu a kasashe daban-daban, inda makarantu a kasashen nahiyar Asiya suka rike mukamin na farko zuwa na biyar, a yayinda makarantu a Afrika suke jan baya.

Singapore ce ta farko, sai Hong Kong ta biyu, Koriya ta Kudu ta uku, sai Japan ta hudu a yayinda Taiwan ta rike matsayin na biyar.

Abin mamaki Biritaniya ce ta 20 a duniya a yayinda Amurka ke matsayin na 28.

Kasar Ghana ce ta karshe a cikin jerin kasashe 76 da aka gudanar da bincike a kansu.

Kwararru a kungiyar hadin kai ta fanin tattalin arziki da kuma bunkasa ci gaba a duniya- OECD ne suka yi binciken a kasashe 76 amma ban da Nigeria a ciki.

Jami'i a OECD, Andeas Schleicher ya ce "A karon farko an yi amfani da wani mizani wajen gano ingancin ilimi a kasashen duniya."

An gwada yara 'yan shekaru 15 ne a fannin lissafi da kimiya:

  • Singapore
  • Hong Kong
  • Koriya ta Kudu
  • Japan
  • Taiwan
  • Finland
  • Estonia
  • Switzerland
  • Netherlands
  • Canada