Mutane 67 sun mutu a girgizar kasa ta biyu a Nepal

Hakkin mallakar hoto
Image caption Al'umomin kasar Nepal na bukatar agaji

An ci gaba da aikin ceton jama'a a kasar Nepal wacce ta sake gamuwa da bala'in girgizar kasa karo na biyu a kasa da makonni uku.

Jami'ai a kasar suka ce har yanzu suna kokarin tantance girman ta'adin da girgizar kasar ta biyu ta yi, inda suka ce akwai mutane da burabuzan gine gine suka birne.

Kawo yanzu kimanin mutane 50 ne aka tabbatar da mutuwar su a Nepal, da kuma wasu 17 a arewacin India sakamakon girgizar kasar karo na biyu.

Hukumomi sun ce suna sa ran adadin mutanen da suka mutu ya haura cikin sa'o'i masu zuwa.

Mutane da yawa a kasar sun sake kwana a waje saboda fargabar kwana a cikin gidaje.

Kungiyoyin bada agaji su ka ce girgizar kasar ta biyu ta mayar da hannun agogo baya a aikin bada tallafi ga mutanen da bala'in girgizar kasan na farko ya shafa wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 8000.