An kashe mutane sama da 40 a Pakistan

Hakkin mallakar hoto Reuters

Jami'ai a Pakistan sun ce an kashe mutane 43 a wani hari da aka kai kan wata motar da ke dauke da 'yan Shi'a a birnin Karachi.

wasu mutane dauke da bindigogi a kan babura ne suka zagaye motar safar, sannan suka bude wuta kan mai-uwa-da-wabi

Rahotanni na cewa fasinjoji da dama da sun samu raunuka, wasu ma na cikin mawuyacin hali.

An yi ammanar cewar mutanen da ke cikin motar safar za su kai sittin, da suka hada da mata da kuma kananan yara.